Majalisar dinkin duniya zata dauki mataki a Syria

MDD a Syria

Majalisar dikin duniya zata janye ma'aikatanta wadanda ayyukansu ba dole ba ne, daga kasar Syria, saboda yadda rikici ke kara kamari.

Wani kakakin Majalisar dinkin duniya, Martin Nesirky ne ya bada sanarwar hakan.

Inda ya ce Majalisar zata dakatar da ayyukan da take gudanarwa a cikin kasar, har zuwa wani lokaci nan gaba.

Ma'aikatan da yawan su ya kai ashirin da biyar, daga cikin kimanin dari ne zasu bar kasar a wannan mako.

Tarayyar Turai ma zata janye nata ma'aikatan.

Tun daga farkon wannan rikici, watanni ashirin da suka wuce, Majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyi na kasashen duniya ke bada agaji ga dubban 'yan kasar ta Syria.

Majalisar dinkin duniya ta ce an kashe ma ta ma'aikatan takwas a wannan tsakanin.