Amurka ta yi kira ga Israila kan gina matsugunan Yahudawa

Amurka ta yi kira ga Isra'ila ta sake nazarin shirin ta na gina dubban matsugunan Yahudawa, a Gabar yamma da Kogin Jordan da gabashin birnin Kudus.

Kakakin Fadar gwamnatin Amurkar, Jay Carney ya kira wannan yunkuri a matsayin koma-baya ga kokarin da ake yi na samun zaman lafiya da Palasdinawa.

Kasashen Turai da dama da suka hada da Faransa da Birtaniya sun kira jakadun Isra'ila don kokawa game da shirin.

Sai dai Isra'ilar ta yi watsi da sukar da kasashen duniya ke yi ma ta, tana cewa za ta cigaba da tsayawa kan biyan bukatun ta masu muhimmanci.

Karin bayani