Sojin Rwanda sun taimakawa M23-MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka kwarmata ya ce, sojojin Rwanda suna da hannu dumu-dumu, a mamayar da 'yan tawaye suka yi wa garin Goma na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Rahoton wanda aka tattara wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, sojojin Rwanda kimanin dari biyar ke tare da 'yan tawayen na kungiyar M23, a lokacin da suka kai harin.

Wani mai magana da yawun sojojin na Rwanda Brigediya Janar Joseph Nzabam-wita ya gaya wa BBC cewar wannan zargi ne mara makama.

Dakarun Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo dai sun koma Goma ranar Litinin, kwanaki biyu bayan da 'yan tawayen suka janye daga birnin.

Sai dai wannan rahoton na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi futar ba zata ya samu kakkausar suka daga gwamnatin kasar Rwanda.

'Yan tawayen dai wadanda suka janye daga birnin Goma sun yi dandazo ne a wajen birnin, kuma sun ci alwashin sake kwace birnin matsawar gwamnatin Congo bata cika alkawarin ta ba.

A baya dai an zargi kasar Rwanda da hannu a rikicin na Congo, abin da gwamnatin Rwandan ta ke musantawa.