'Yan adawa a Nijar sun yi watsi da kasafin kuɗi

Shugaba Mahammadou Issoufou
Image caption kasafin kuɗi na 2013 ya janyo cece kuce a Nijar

A Jamhuriyar Nijar 'yan majalisar dokokin ƙasar su ka yi na'am da sabon kasafin kuɗi na shekarar 2013 wanda ya tashi miliyan dubu ɗaya da ɗari uku da talatin da ɗaya na cefa.

Sai dai 'yan adawa a majalisar ba su amince da shi ba, su na masu cewa akwai saɓani tsakanin kasafin kuɗin da tsarin da gwamnatin ta yi na bunƙasa tattalin arziki da kyautata jin daɗin rayuwar al'umma PDES da ta yi na'am da shi wanda kuma shi ne zai kasance alƙiblarta dangane da duk wasu ayyukan da za ta yi daga 2012 zuwa 2013 Daga yamai wakilinmu baro arzika ya aiko da wannan rahoton

Kakakin 'yan adawar Alhaji Tijjani Abdilkadir ya shaida wa BBC cewa sun yi hakanne ganin kasafin kuɗin na bara ma , gwamnati bata haɗa ko kashi hamsin cikin ɗari ba.

'Yan adawar sun kuma soki matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na kashe maƙuden kuɗaɗen gwamnati wajen sayen jirage guda biyu, a madadin yiwa talakawa aiki a cewar su.

To sai dai Alhaji Abdulmuminu Ghusman na jam'iyyar PNDS ya kare wannan zargi inda ya ce za a sai jirgin farko ne saboda zurga zurgar shugaban ƙasa da duk wanda zai fita daga Nijar.

Jirgi na biyu kuwa a cewar sa, jirgi ne da za a yi amfani da shi wajen harkokin tsaro a ƙasar