Obama ya gargadi Syria kan makamai masu guba

Shugaba Obama na Amurka ya gargadi Shugaban Syria Bashar al-Assad ya guji yin amfani da makamai masu guba sakamakon wani rahoto na hukumar leken asiri ta Amurka wanda ya nuna cewar akwai yiwuwar ana shirye-shiryen amfani da makaman.

Mr Obama yace duniya na kallo, kuma gwamnatin za ta dandana kudar ta idan ta yi amfani da wadannan makamai a kan mutanen ta.

Ya kara da cewa ba za a lamunci amfani da makamai masu guba ba.

Ba bu karin haske sosai a kan lamarin, amma wani Jami'i a Amurka wanda ba a bayyana sunansa ba yayin da yake magana da New York Times ya yi jawabi kan abin da ya kira yiwuwar shirin amfani da makamai masu guba.

Mai magana da yawun Shugaba Obama, a fadar White House, Jay Carnel, ya ce damuwa na karuwa kan yiwuwar gwamnatin Assad ta yi amfani da makamai masu guba.

A Damascus kuwa Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta ce ko da tana da irin wadannan makaman, ba za ta yi amfani da su kan al'ummar ta ba, ko wane irin yanayi ta tsinci kanta a ciki.