An kashe yara masu yawa a Syria

Syria
Image caption Faɗa na cigaba da ƙazanta a Syria

Yayinda yaƙin basasa ke ƙara ƙamari a Syria, dukkan ɓangarorin na cewa an kashe wasu yara masu yawa, bayan da aka yi harbi da iggwa kan wata makaranta dake wajen birnin Damascus.

Kafafen yaɗa labaran hukuma a Syriar na cewa mutane kimanin talatin ne suka mutu, kuma kusan dukkansu ƙananan yaralokacin da dakarun 'yan tawaye suka buɗe wuta kan makarantar a wani sansanin 'yan gudun hijira.

Sai dai kuma su ma 'yan tawayen na ɗora alhakin harin ne a kan dakarun gwamnati.

Faɗa , da kuma kai hare haren bam sun ƙara tsananta a kewayen birnin Damascus a 'yan kwanakin nan, yayinda sojojin gwamnati ke ƙoƙarin hana dakarun 'yan tawaye isa tsakiyar babban birnin ƙasar.

Karin bayani