'Yan wasan Eritrea sun nemi mafakar siyasa a Uganda

Image caption Tutar kasar Eritrea

'Yan wasan kwallon kafa na kasar Eritrea su goma sha takwas wadanda suka yi batan dabo a kasar Uganda ranar lahadi sun kai kansu ga hukumomi suna neman mafakar siyasa a kasar.

David Apollo Kazungu kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun hijira a ofishin Farayin Ministan kasar ya shaidawa BBC cewar 'yan wasan sun tuntube shi ranar laraba inda suka nemi mafakar siyasa.

'' Sun fada mana cewar halin da kasar take ciki baya da kyau kuma muna duba halin da suke ciki da kuma takardun da suka kawo mana. Amma dai za su ci gaba da kasancewa a hannunmu tun da sun yi rijista.'' inji shi.

'Yan wasan 17 da likitansu sun buya ne ranar Lahadi bayan da su ka ce za su fita sayayya, inda jami'ai biyar da 'yan wasa biyu kawai suka koma Eritrea ranar Talata.

Hakan ta taba faruwa a shekarar 2010 bayan kammala wasan Cecafa a Tanzania, 'yan wasa goma sha uku daga cikin 'yan wasan Eriteria sun bace tare da sauya sheka.

Da yawa daga cikin wadannan 'yan wasa sun kare a biranen Houston da kuma Texas a karkashin shirin Amurka na 'yan gudun hijira.

Karin bayani