Dubban mutane sun yi bore a fadar Masar

Image caption Masu zanga-zanga a fadar Masar

Dubun-dubatar mutanen dake adawa da Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi, sun shiga wata zanga-zanga da aka yi a kusa da Faadar Shugaban kasar dake birnin Alkahira.

A wani sashin fadar, 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye, don korar masu zanga-zangar baya wadanda suka tsallaka wasu wayoyi da aka kare yankin da su.

Jami'an tsaro sun ba da sanarwa ta talabijin cewa Shugaba Morsi ya fice daga cikin ginin, tare da yin kira gare su da su kwantar da hankulansu.

Masu zanga-zangar sun ce ba su goyi bayan dokar da Shugaban kasar ya kafa ba, wadda ta ba shi wasu sababbin jerin iko da kuma daftarin kundin tsarin mulkin nan dake tattare da cece-kuce.

Zanga-zangar dai ta dau zafi a kasar ta Masar inda masu adawar suka ci alwashin za su ci gaba da boren sai baba ta gani.

Sanarwa

Talabijin a kasar ta rawaito jawabi daga Dakarun Jami'an tsaron kasar, su na kira ga masu zanga-zangar kada su tada hankali.

Sanarwar dai ta ce Jami'an tsaron sun janye zuwa wajen katangar fadar shugaban kasar, bayan da masu zanga zangar suka cire wayoyin da suka zagaye yankin.

An kuma tabbatar da cewa Shugaban kasar ya bar fadar bayan ya kare wani zaman taro.

A wata sanarwar kuma da masu adawa da Shugaban suka fitar, suna kira da ayi zaman dirshen a fadar shugaban kasar da kuma dandali daban-daban a kasar har zuwa ranar Juma,a.

Wakilin BBC a Alkahira ya ce, "ko lokacin da aka yi zanga-zangar da ta hambarar da tsohon Shugaban Kasar Hosni Mubarack ba a killace fadar ba kamar wannan karon ba.