NAPTIP ta kubutar da matan Najeriya 50

naptip
Image caption Matan da ake safararsu zuwa kasashen waje

Hukumar yaki da masu safarar mutane a Najeriya wato NAPTIP ta ce ta kubutar da wasu mata 'yan Najeriya su hamsin da aka tilasta musu shiga karuwanci a kasashen Ghana da kuma Code' d Voire.

A cewar ta, matsalar ta soma bazuwa zuwa wasu sassan Kasar da ba'a saba jin sunayensu ba, saboda akwai jihohin da matsalar tafi kamari.

Jami'an hukumar NAPTIP sun ce wasu jama'a ne suka yodari matan suka ketara dasu kasashen waje don zammar samar musu aikin yi.

Wani jami'in NAPTIP ya shaidawa wakiliyar BBC, Raliya Zubairu cewar a yanzu ana samun matan da ake safararsu daga jihohin Nasarawa da Anambra, jihohin da a baya ba a samun wadanda ake kaiwa kasashen waje don suyi karuwanci.

Karin bayani