Rafael na bukatar goyon bayan Chelsea - Avram

Manajan Chelsea na wucin gadi, Rafael Benitez
Image caption Manajan Chelsea na wucin gadi, Rafael Benitez

Tsohon manajan kulob din Chelsea, Avram Grant ya nemi 'yan wasan su baiwa mai horar da 'yan wasa na wucin gadi, Rafael Benitez hadin guiwa.

Masoya kulob din Chelsea da dama ne suka yi wa Benitez ihu, a fitowarsa ta farko a wasansu na gida.

Sai dai Grant da kulob din na Chelsea sun musanta cewa Avram din zai koma ya cigaba da aiki tare da Benitez.

Grant ya shaidawa BBC cewa " Abu mafi muhimmanci da yakamata su sani shi ne, suna da mai horar da su kuma yana bukatar hadin kansu. "

Dan shekaru 57 ya yi amanna cewa kamata ya yi masoya kulob din su marawa Benitez baya ganin halin da kulob din ya tsinci kansa, maimakon neman a sauya shi.

A watan Oktoba kulob din na sama a gasar premier League da maki hudu, amma yanzu ya koma bayan Manchester United da maki goma.

Chelsea ta buga wasanni bakwai ba tare da samun nasara ba.