Shugaba Morsi ya yi kiran a tattauna

Masar
Image caption An shirya gudanar da zanga-zanga a ranar Juma'a

Shugaba Muhammad Morsi na kasar Masar ya yi kiran tattauna wa da 'yan adawa domin kashe wutar rikicin siyasar da ta dabaibaye kasar.

Fada tsakanin masu adawa da magoya bayan Mr Morsi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar tare da jikkata wasu 644 a cikin dare.

A jawabin da yayi wa al'ummar kasar ta gidan talabijin, Mr Morsi ya nuna alhinisa kan wadanda suka rasa rayukansu a tarzomar.

Ya ce yana goyon bayan zanga-zangar lumana, sai dai ya ce an biya wasu mutane kudi domin su haifar da rikici a kasar

Karin bayani