Masar na cikin rudanin siyasa

Shugaba Muhammad Morsi
Image caption Shugaban kasar Masar

Magoya baya da kuma masu adawa da shugaba Muhammad Morsi na ci gaba da zanga zanga a sassa daban daban na kasar Masar.

Sojoji sun kori masu zanga zanga a kusa da fadar shugaban kasa, sun kuma killace kewayen fadar shugaban kasar a birnin Alkahira, inda aka yi wani mummunan rikici jiya Laraba da dare.

Tuni wasu masu zanga zangar suka sake komawa wurin suna kira ga shugaba Morsi da ya sauka daga mulki.

Ahmad Saleh al-Aswany daya daga cikin ,yan adawa ya ce Muhammad Morsi ya raba kan kasa, kuma hakan ba zata yiwu ba.

Mafitar wannan rikicin ita ce ta soke wannan doka.

Al'umar kasar ta Masar na jiran wani jawabi da shugaban kasar zai gabatar ga al'umar kasar, inda zai bayyana matsayinsa, kodayake ana samun jinkiri wajen yin hakan.

Karin bayani