An tuhumi tsohon Fira Ministan Thailand da laifin kisan kai

Zanga Zanga a Thailand
Image caption Ana tuhumar Abhisit Vejjajiva

An tuhumi tsohon Fira Ministan Thailand, Abhisit Vejjajiva da laifin kisan kai, kan mutuwar wani direban tasi a lokacin zanga zangar gama-garin da aka yi ta nuna adawa da gwamnatinsa a 2010.

Wannan tuhuma da aka yi wa Mr Abhisit da mataimakinsa, ita ce karon farko da aka ta…ďa zargin wasu jami'ai, tun bayan mummunan tashin hankalin da aka yi da magoya bayan wani tsohon Fira ministan, Thaksin Shinawatra.

Tharit Pengdit darakta ne a ma'aikatar bincike ya kuma ce sun amince su tuhumi Abhisit Vejjajiva, tsohon Fira Ministan, da mataimakinsa saboda su, su ka bada umarnin a yi amfani da harsasai masu kisa.

An kashe mutane sama da tamanin a tashin hankalin.

Karin bayani