An raunata shugaban hukumar leken asirin Afghanistan

Taswirar kasar Afganistan
Image caption Taswirar kasar Afganistan

An raunata shugaban hukumar leken asirin Afghanistan, Asadullah Khalid a wani hari da wani dan kunar bakin wake da ya yi shigar burtu a matsayin jakadan wanzar da zaman lafiya ya kai masa.

Mr Khalid yana ganawa ne da mutumin da ya kai masa harin a wani gida a Kabul inda aka shirya zasu tattauna batun sasantawa tsakanin Taliban da gwamnatin kasar ta Afghanistan.

Jami'ai sun ce raunukan da ya ji suna da muni amma basa barazana ga rayuwarsa.

Kungiyar Taliban ta ce ita ce ta kai harin kan Malam Khalid, wanda babban na hannun daman shugaba Karzai ne.

Shugaba Karzai din ya yi Allah wadai da harin tare da fatan jami'in zai sami sauki