An nemi haɗin kan ƙasashe kan Syria

Ban Ki-moon
Image caption Ban Ki-moon

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki- moon ya buƙaci ƙasashe wakilan kwamitin sulhun Majalisar da su hada kai a matsayinsu kan rikicin Syria.

Rasha da China sun sha nuna adawa da matsayin ƙasashen Yammacin duniya.

Mr Ban na magana ne a Turkiya a rana ta biyu ta rangadin da yake yi a ƙasashen da rikicin Syria ya shafa.

Ya kuma bi sahun masu gargadi na baya bayan nan ga gwamnatin Syriar da kada ta yi amfani da makamai masu guba a kan mutanenta.

Mr Ban ya kuma yi kira da a gaggauta taimaka wa 'yan gudun hijira daga rikicin.

Karin bayani