Makarantar koyawa karnuka tukin mota

Karnuka
Image caption Tuni har karnukan sun fara koyar dabi'ar tukin ganganci

Wata kungiyar kula da dabbobi a kasar New Zealand, ta fara koyawa wasu karnuka uku yadda za su tuka mota.

Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne domin nuna irin basirar da dabbobi keda ita, da kuma dalilin da ya kamata a rinka basu kulawa ta musamman.

Karnukan, Monty, da Ginny, da Porter, sun shafe makonni bakwai da suka gabata suna koyan hanyoyi goma da za su basu damar koyon yadda za su kunna mota da sauya giya da rike sitiyari.

Kungiyar ta New Zealand wacce ta dauki nauyin shirin, ta ce tana fatan karnukan uku za su samu damar nuna basirar da suka koya a wani shirin talabijin da za a watsa kai tsaye a karshen mako.

Mark Vette, wani mai kula da dabbobi, ya ce wajibi ne mu cimma burinmu, "lokaci yayi da za mu nuna cewa karnuka za su iya tuka motoci.'

Mr Vette ya kara da cewa tuni har karnukan sun fara koyar dabi'ar tukin ganganci.

"Kwanaki kadan da suka gabata, motar na tafiya a guje, saura kiris su bi takan malamin na su," a cewarsa.