Khaled Meshaal ya ziyarci zirin Gaza

Khaled Meshaal
Image caption Da isarsa birnin, ya yi sujjada domin nuna godiya ga Allah

Shugaban siyasa na kungiyar Hamas, Khaled Meshaal ya bayyana ziyararsa ta farko zuwa zirin Gaza da cewa kamar ranar da aka "sake haihuwarsa karo na uku".

Sauran ranakun haihuwar ta sa "guda biyu" su ne ranar da ya tsira daga yunkurin kisan gilla daga Isra'ila a Jordan a shekara ta 1997, da kuma ainahin ranar haihuwarsa ta 1956.

Mr Meshaal ya shafe shekaru 45 ba tare da ya sanya kafarsa a yankin Falasdinawa ba.

Ziyarar tasa ta biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma wacce ta kawo karshen kwanakin da aka shafe ana tashin hankali tsakanin Isra'ila da Hamas .

Kungiyar ta Hamas na rike da iko da Gaza tun shekara ta 2007.

Mr Meshaal ya shiga Gaza ne daga kasar Masar ta kan iyakar Rafah, inda ya yi sujjada domin nuna godiya ga Allah.

Jami'ai sun ce matarsa ta isa yankin tun ranar Alhamis.

A jawabin da ya yi ga manema labarai, ya ce: "Ina ganin wannan lokaci kamar ranar da aka haife ni karo na uku, kuma na roki Allah ya sanya ranar haihuwa ta hudu ta kasance ranar da dukkan Falasdinawa za su samu 'yancin kai."

"A kodayaushe zirin Gaza na cikin zuciyata," a cewarsa.