Ana zaben shugaban kasa a Ghana

Zabe a kasar Ghana
Image caption Zabe a kasar Ghana

Al'ummar kasar Ghana na jefa kuri'a domin zaben sabon shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin.

Masu lura da al'amura dai na ganin za a fafata ne a zaben tsakanin manyan 'yan takara biyu, wato shugaba mai ci , John Dramani Mahama da Nana Akufo Addo, dan mutumin da ya shugabanci kasar a farkon shekarun 1970.

Shugaba Mahama dai yana neman cikakken wa'adinsa na farko ne na mulki bayan da ya karbi mulki a watan Yuli sakamakon mutuwar wanda ya gada John Atta Mills.

'Yan takarar shugabanci guda takwas ne dai za su fafata ciki har da dan takarar independa guda daya.

Hukumar zaben kasar dai ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaben kuma ta aika da kayan aiki zuwa dukkan sassan kasar.

Za a fara zaben ne daga karfe bakwai na safe agogon Ghana zuwa karfe biyar na marece.