McAfee bai kamu da cutar bugun zuciya ba- Lauya

John Mcafee a Guatemala, Belize
Image caption John Mcafee a Belize

Lauyan attajirin Ba'amurken nan mai yin manhajar kwamfuta, John McAfee, ya ce liktoci sun sheda masa cewa, Mr McAffen bai samu ciwon bugun zuciya ba kamar yadda rahotanni ke cewa a baya.

Lauyan Mr Telesforo Guerra yace, ya ce Mr McAfee ya gamu da matsala maras tsanani har sau biyu, inda da bugun jininsa ya hau abinda ya sa zuciyarsa ta rika bugawa da sauri.

Rahotannin farko game da batun lafiyar Mr McAfee din na zuwa ne sa'oi hudu bayan da kasar Guatemala ta yi watsi da bukatunsa na neman mafaka.

Mahukuntan kasar ta Guatemalan sun cafke shi ne saboda abinda suka bayyana shiga kasar ba ta haramtacciyar hanya, suka kuma yi aniyar tasa keyarsa makwabciyarta Belize, inda ake neman sa ruwa a jallo domin amsa wasu tambayoyi game da zargin aikata kisan kai da ake yi masa.

Mr McAfee dai ya zargi gwamnatin ta Belize ta yunkurin dora masa alhakin kisan kan da yace bai aikata ba.