Ana ci gaba da kirga kuri'a a zaben Ghana

Zabe a Ghana
Image caption Zabe a Ghana

A kasar Ghana ana ci gaba da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin da aka gudanar a jiya. Yau ma sai wasu suka yi zaben.

Sai dai kuma anyi wannan zabe ne cikin lumana a mafi yawan wurare.

Fafatawa dai ta fi zafi ne tsakanin shugaba mai ci, John Dramani Mahama da kuma Nana Akufo-Addo na jam'iyyar adawa ta NPP.

Wasu rahotanni sun ambaci jam'iyyar adawa ta NPP na cewa dan takararta ne zai samu galaba a zaben, yayinda aka dauki matakan tsaro a kewayen hukumar zabe.

Tuni dai wasu suka fara hasashen cewa mai yiwa sai an kai ga zagaye na biyu na zaben.

Sakamako na nuna cewa manyan yan takarar biyu na tafiya kafada da kafada.

Karin bayani