An Jinkirta zaben shugaban kasa a wasu sassan kasar Ghana

Zaben kasar Ghana
Image caption Zaben kasar Ghana

A kasar Ghana an jinkirta zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki a wasu wurare, domin baiwa dubban masu zaben da basu samu damar kada kuri'unsu ba a jiya damar yin zaben.

Da safiyar nan ne za a cigaba da zaben a wasu wuraren da aka gamu da matsaloli.

Matsalar na'urar kwamfutar dake daukar hoton yatsu wadda ake amfani da ita a zaben ta haifar da dogayen layuka.

Duk da wannan masu sanya ido a zaben na cikin gida sun ce ba a sami wasu manyan matsaloli ba wajen gudanar da zaben.

Ana dai saran za a yi kan-kan-kan ne a zaben tsakanin manyan 'yan takara biyu, shugaba mai ci John Dramani Mahama da jagoran 'yan adawa, Nana Akufo-Addo.

Sai dai kuma wasu 'yan kasar na ganin duk da yadda ake kankankan din za a samu gwani a zagayen farko.