An kara tsawon yarjejeniyar Kyoto zuwa 2020

Wakilai a taron Doha kan sauyin yanayi.
Image caption Wakilai a taron Doha kan sauyin yanayi.

Kusan kasashe dari biyu dake halartar taron majalisar dinkin duniya a kan sauyin yanayi a Qatar sun amince su tsawaita yarjejeniyar Kyoto a kan yaki da dumamar yanayi zuwa shekara ta 2020.

Yarjejeniyar ta Kyoto dai zata zo karshe ne a karshen wannan shekarar.

An cinma yarjejeniyar ta yau ce bayan karin sa'o'i ashirin da aka samu ana tattaunawa a kokarin shawo kan kasashe masu arziki su biya diyya ga kasashe matalauta kan asarar da suka tafka sakamakon sauyin yanayin.

An kai ga wannan matsayi ne bayan da aka shafe kwanaki goma sha biyu ana ta tafka muhawara mai zafi.

Yarjejeniyar ta shafi kashi sha biyar ne kawai cikin dari na yawan gurbatacciyar iskar da ake fitarwa a duniya, saboda wasu karin kasashen sun fice daga cikinta; Kuma a yanzu ma matakin da aka dauka na wucingadi ne, wanda aka dauka da nufin share fage na wata yarjejeniyar da da ta fi wannan girma wadda za a tattauna kanta a kuma amince da ita daga nan zuwa 2015.

Sai dai duk da haka yarjejeniya ce wadda za a yi aiki da ita bisa tasri na dokoki.

Tun yanzu ann kara wa'adin aikin yarjejeniyar Kyoto kan sauyin yanayi zuwa 2020, ana yi wa matakin kallon wani muhimin yunkuri a hanyar da aka dauka mai sarkakiya da wuyar bi ta yaki da dumamar yanayi a duniya.