Sojoji sun ja kunnen 'yan siyasa a Masar

Masu zanga zanga a Masar
Image caption Masu zanga zanga a Masar

Rundunonin sojan Masar sun yi kashedin cewa, wani mummunan abu zai iya biyo baya idan har bangarorin siyasar kasar dake adawa da juna ba su warware takaddamar dake tsakaninsu ba ta hanyar tattaunawa.

A wata sanarwa da aka watsa ta gidan tabijin din kasar, kakakin rundunonin sojan Masar din yayi kashedin cewa, ba zasu lamunci cigaba da tashin hankali a kasar ba.

Mai karanta labarai a gidan tabijin kenan tana karanto sanarwar sojan Masar din dake jaddada cewa, matsayinsu shi ne tattaunawa ita ce kadai hanyar warware dambarwar siyasar kasar ta Masar.

Wannan jan kunne da sojan Masar din suka yi na zuwa ne bayan 'yan adawa a Masar din sun yi kira ga Shugaba Muhammad Morsi ya janye matakin da ya dauka na baiwa kansa gagarumin iko.

Dubban masu zanga zanga ne suka yi dafifi a kofar fadar shugaban kasa a birnin Alkahira, tun cikin dare har wayewar gari, bayan da suka keta wasu shingayen tsaro da aka kafa, inda suka yi watsi da da kiran da shugaba Morsi yayi na tattaunawa.

Rahotanni daga Alkahira na cewa Shugaba Muhammad Morsi na ganawa shugabannin jam'iyyu da wasu kusoshin gwamnati.

Karin bayani