Za a yiwa Shugaba Chavez aikin tiyata a Cuba

Image caption Hugo Chavez, shugaban Venezuela

Ministan yada labaru na Venezuela ya ce tawagar likitocin dake duba lafiyar shugaba Hugo Chavez a Cuba, sunce suna da tabbaci game da nasarar aikin tiyatar da za a yi masa, saboda cutar sankara ( wato cancer ) dake damunsa.

A wata sanarwa da aka watsa a gidan talabijin na kasar, Ernesto Villegas ya nemi 'yan kasar ta Venezuela da su yi wa shugaban addu'a, wanda yake shirin fuskantar aikin tiyata.

Chavez ya ce zai mika mulki ga mataimakinsa, Nicolas Maduro, idan har ya kasance ba zai iya komawa kan kujerar sa ba.

Shugaban Kasar Ecuador Rafeal Correa wanda ya ziyarci Shugaba Chavez a asibiti tun da farko, ya bayyana fatan samun lafiyar takwaran aikin- nasa.