Masar: 'Yan adawa sun ce zasu ci gaba da bore

Image caption Muhammad Morsi, shugaban Masar

'Yan adawa a Masar sun ce, zasu ci gaba da nuna bore da yin zanga-zanga cikin makonnin dake tafe domin nuna rashin amincewarsu da yin zaben raba gardama akan daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar dake janyo cece kuce.

'Yan adawar dai suna so ne shugaba Morsi ya dakatar da kuri'ar raba gardama akan kundin tsarin mulkin kasar da ake cece-kuce akansa.

Tun daga lokacin da shugaba Muhammad Morsi ya bayyana baiwa kansa gagarumin iko a watan Nuwamba ne kawunan al'ummar Masar suka kara rarrabuwa, kuma kasar ta rika fuskantar tashin hankali.

Tuni dai shugaba Morsi ya janye dokar da ta ba shi gagarumin iko wajen tafiyar da mulkin kasar.

Sai dai bisa ga dukkan alamu 'yan adawa ba su gamsu da wannan mataki ba.

Koda jiya dai sai da rundunonin sojan kasar suka yi kashedin cewa, ba zasu cigaba da sa ido suna kallo ana tashin hankali a kasar ba.