Al Bagdadi Al Mahmoudi ya gurfana a gaban kotu

Tsohon Fira Ministan Libya
Image caption Ana yiwa Tsohon Fira Minista Shari'a a Libya

An tuhumi tsohon Fira Ministan libya Al Bagdadi Al Mahmoudi a Tripoli babban birnin kasar.

Ana zargin Mr Al Mahmoudi da kuma wasu mutum biyu da alhakin aikata wasu abubuwa da su kai sanadiyyar mutuwar Libyawa da dama

Ana kuma zargin su da karkatadda kuɗaɗen al'umma da su ka tasamma kusan dala miliyan ashirin da biyar zuwa wasu bankuna a Tunisia

Mr Al Mahmoudi wanda ya tsere zuwa Tunisia bayan an kifar da gwamnatin Kanal Gaddafi, shine babban jam'in gwamnatin data shuɗe na hudu mafi girma da ake tuhuma a Libya