Ana yunkurin gano mahaifiyar Ngozi

Ministar kudin Nijeriya Ngozi Okonjo Iweala
Image caption Sace mutane domin neman kudin fansa ba bakon abu bane a Najeriya

HRundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta dukufa wurin gano wadanda suka sace Farfesa Kamene Okonjo, mahaifiyar ministar kudi ta kasar Ngozi Okonja-Iweala.

Farfesa Kamene Okonjo mai shekaru 82 da haihuwa, an yi awangaba da ita ne a gidanta da ke jihar Delta a Kudu maso Kudancin kasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar kudi ta Najeriya ya ce an yiwa Ngozi Okonja-Iweala barazana a baya-bayan nan, amma bashi da tabbas ko wannan na da alaka da barazanar da aka yi mata.

Najeriya na sahun gaba-gaba a duniya wurin sace mutane domin neman kudin fansa.

Wannan mummunar sana'a dai na samar da makudan kudade ga masu yinta.

Wadannan miyagun laifuka dai sun fi faruwa ne a Kudancin kasar, sai dai lamarin kan ritsa da mutane da yawa a sassan kasar da dama.

Karin bayani