An yi musayar wuta a garin Potiskum

Sambo Dasuki, Mashawarci kan harkokin tsaro a Nijeriya
Image caption Sambo Dasuki, Mashawarci kan harkokin tsaro a Nijeriya

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jihar Yobe, a gabashin Nigeria ta ce mutane kimanin goma sha hudu ne suka hallaka ciki har da wani jami'in 'yan sanda, a harin da wasu 'yan bindiga suka kai wani a ofishin 'yan sanda dake garin Potiskum a jiya.

Mazauna garin sun ce sun kwana cikin zulumi sakamakon karar fashewar wasu abubuwa da harbe-harben bindigogi da tsakar dare, har zuwa wayewar garin yau.

Jihar Yobe dai na daya daga cikin jihohin dake gabashin kasar dake fama tashe tashen hankula sakamakon hare haren da ake zargin kungiyar ahlus suna lida'awati wal jihad da fi sani da boko haram da kaiwa.

An ambaci kakakin rundunar tsaron, Laftanar Lazarus Eli yana cewar wasu mazauna garin na Potiskum ne suka tuntube suka shaida masu halin da ake ciki, kafin su tura karin dakaru.

Ya kara da cewar jami'insu ya rasu ne a asibiti, sakamakon raunukan da ya samu, sun kuma gano gawarwakin maharan uku, yana mai cewar su kuma sauran wadanda suka tsira sun gudu da sauran gawarwakin maharan.

Wasu mazauna garin sun ce an kona wani banki.

Karin bayani