Amurka ta ci tarar bankin HSBC dala biliyan 2

Image caption hsbc bank britain

Rahotanni daga Amurka sun ce bankin HSBC na Burtaniya zai biya hukumomin kasar makudan kudaden da suka kai dala biliyan daya da miliyan dari tara, don wanke kansa daga zargin halalta kudin haram.

Mai yiwuwa a bayar da sanarawar cimma wannan matsaya yau Talata.

Wakiliyar BBC ta ambato hukumomi suna cewa bankin ya yiwa tsatstsauran takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran karan tsaye sannan kuma ya kyale kungiyoyin fataken miyagun kwayoyi na Mexico sun halalta kudaden haram.

Ranar Litinin babban bankin Amurka ya umarci wani bankin na Burtaniya, Standard Chartered, ya biya dala miliyan dari uku da ashirin da bakwai don wanke kansa daga zargin keta takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran da ma wasu kasashen.