EFCC ta kama dan gwamna Sule Lamido

Sule Lamido
Image caption Sule Lamido ya shafe shekaru sama da biyar yana mulkin jihar Jigawa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ce jami'anta sun kama daya daga cikin 'ya'yan gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido.

Hukumar ta ce an kama babban dan Gwamnan Aminu Sule Lamido bisa zargin sa da yunkurin fita da kudi zuwa kasar waje, sama da yadda dokar Najeriya ta tanada.

Kakakin hukumar EFCC ya shaida wa BBC cewa an kame Aminu Sule ne bayan da ya bayyanawa jami'an shige da fice a filin saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano, cewa yana dauke da kudi dala 10,000.

Amma bayan da aka bincika sai aka ga yana dauke da dala 40,000, wanda ya sabawa yadda doka ta tanada.

Sai dai har kawo yanzu gwamnatin ta jihar Jigawa ba ta ce komai ba dangane da wannan batun.

Batun safarar kudaden haram dai abune da aka dade ana zargin 'yan siyasar Najeriya da yi.

Kuma masu lura da al'amura suna ganin batun yaki da cin hanci da rashawa da kasar take ikirarin yi, ba ya wani tasiri wurin magance irin wadannan matsaloli da ke zubar da kimar kasar a idon duniya.

Karin bayani