Fira Ministan Mali ya yi murabus

Firayim Minista Cheikh Modibbo Diarra
Image caption Firayim Minista Cheikh Modibbo Diarra na Mali

Fira Ministan Mali Cheikh Modibbo Diarra, ya yi murabus sa'o'i kadan bayan da sojoji suka tsare shi bisa umarnin jagoran juyin mulkin kasar Amadou Sanogo.

Wani mai magana da yawun Sojoji a Mali ya ce an kama Firayim Minista Cheikh Modibbo Diarra a gidansa da ke Bamako babban birnin kasar, inda aka tsare shi a wani barikin sojoji.

Mai magana da yawun sojojin ya shaida wa BBC cewa an kama Mista Diarra ne lokacin da ya ke kokarin barin kasar ta Mali zuwa Faransa, ana zarginsa da yunkurin yiwa tsarin dimokradiyya zagon kasa.

Ya ci gaba da cewa an kama Fira Ministan ne bayan samun umarni daga jagoran sojojin, Kyaftin Amadou Sanogo, wanda ya jagoranci juyin mulkin da aka yi a watan Maris, al'amarin da ya jefa kasar cikin rikici.

Mista Diarra dai ya kasance jagoran gwamnatin rikon kwarya ta farar hula wadda ke kokarin dawo da zaman lafiya a kasar.

Karin bayani