Faransa ta yi tir da murabus din Diarra

Sojojin Mali
Image caption Sojojin Mali

Kasar Faransa tayi Allah wadai da abinda ta kira tilastawa Fira Ministan Mali Moddibo Diarra yin murabus, sai dai sojin kasar sun musanta cewa juyin mulki suka yi masa.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Faransan Philip Lalliot yace abinda ya auku na nuni da bukatar da ke akwai na aikewa da rundunar sojin Afirka da za ta daidaita al'amura a Kasar.

Fira Ministan ya taba fadar cewa ya na goyon bayan yin amfani da karfin soji dan kawar da masu fafutukar islama da ke iko da arewacin mali.

A lokacin da aka kama shi ya na kan hanyarsa ta zuwa kasar Faransa ne, wadda take baiwa nahiyar Africa kwarin gwiwa domin shiga tsakani.

Diarra dai ya na jagorantar gwannatin rikon-kwarya don tabbatar da zaman lafiya bayan hambarar da gwamnatin da ta gabata da ta janyo tashe-tashen hankula a kasar a watan maris da ya gabata.

Kakakin sojin kasar Bakary Mariko ya shaidawa BBC cewa wanda ya jagoranci juyin mulkin ya na ganin cewa Praministan ya kasa aikin ne.

Tun da fari kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya yi gargadin cewa rikicin arewacin Mali, inda masu fafutukar islama suke iko da shi ya na haddasa gagarumun tashin hankali a yankin Sahel na nahiyar Afrika.

A ranar Litinin da ta gabata Majalisar dinkin duniya ta bayyana Mali a matsayin kasar da tafi kowacce fuskantar barazanar wargajewa a duniya.

Ana dai sa ran cewa nan ba da dadewa ba ne za a sanar da sunan sabon Praminstan kasar ta Mali idan al'amura suka daidaita.