An bada sammacin kame Sanusi Lamido

Sanusi Lamido
Image caption An dade ana sa'insa tsakanin Majalisa da sauran hukumomin gwamnati

Kakakin Majalisar wakilan Najeriya ya sanya hannu kan takardar bayar da umarnin kame wasu Shugabannin manyan kamfanonin Najeriya 16 ciki harda babban banki CBN da kamfanin mai na NNPC.

Shugaban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi da manajan Daraktan NNPC Andrew Yakubu, na rike da manyan hukumomi mafiya muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya.

Majalisar na zarginsu ne da kin amsa gayyata a gaban kwamiti mai kula da harkokin kudade na majalisar wakilan.

Kwamitin na tuhumarsu ne da kin mika Naira tiriliyan 1 da miliyan 3 na kudaden shiga, zuwa asusun gwamnati.

Batun tsaida kasafin kudi a Najeriya na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin bangaren zartarwa da kuma na Majalisun dokokin jihar.

'Muma a jaridu muka gani'

Mai magana da yawun Kakakin Majalisa Malam Imam Imam, ya shaida wa BBC cewa sun fara gayyatar wadannan kamfanoni makonni biyun da suka gabata da su bada bayanai dalla-dalla game da shigowa da kuma kashe kudaden da suka yi a shekara mai fita, amma kuma daga bisani hakan bai samu ba.

A dalilin hakane suka dauki matakin sa hannu a kan wata takarda ta karshe ta sammaci bisa ga yadda doka ta tsara, a cewar Malam Imam Imam.

Yunkurin da BBC ta yi na jin tabakin babban bankin na Najeriya CBN ya ci tura, saboda kakakin bankin bai amsa wayarsa ba.

Sai dai kamfanin NNPC ya ce bai samu takardar sammacin ba. "Muma a jaridu muka gani kamar kowa" a cewar kakakin kamfanin Dr Umar Farouk.

Batun zartar da kasafin kudi tsakanin Majalisa da bangaren zartarwa dai batu ne da ake kai ruwa rana tsakanin bangarorin biyu.

Kuma da alama dai za a ci gaba da abin da za a kira sabon salon zance irin na kurma da bebe tsakanin bangarorin.

Karin bayani