Ana cigaba da zanga - zanga a Masar

Masu adawa da shugaba Morsi a masar
Image caption Masu adawa da shugaba Morsi a masar

Magoya baya da masu adawa da Shugaba Muhammad Morsi na Masar na ci gaba da zanga zangar hamayya da juna gabanin kuri'ar raba gardamar da za'a gudanar ranar asabar a kan daftarin wani sabon kundin tsarin mulki.

A jiya dai masu zanga zangar kin jinin Gwamnati sun keta shingayen da ke kewaye da fadar Shugaban kasar.

Babban hafsan sojin kasar ya bukaci dukkanin bangarorin al'ummar Masar su hadu a yi wata tattaunawa ta kasa domin sasantawa yau Laraba.

Karin bayani