Rana ta biyu ta zanga - zanga a Plato

Zanga - zangar ma'aikata a Najeriya
Image caption Zanga - zangar ma'aikata a Najeriya

A yau ne ake shiga rana ta biyu ta yajin aikin gama-gari na sai baba-ta-gani da kungiyoyin kwadago na Nijeriya suka kira a fadin jhar Filato domin nuna goyon baya ga ma'aikatan kananan hukumomin jihar, wadanda suka yi wata da watanni suna yajin aiki don neman a biya su mafi karancin albashi.

A jiya dai bankuna da sauran wuraren harkoki na yau da kullum sun kasance a rufe a sassa daban-daban na jihar; a wasu yankunanan kananan hukumomin ma har kone-konen dukiya aka yi ciki har da gidajen wasu jami'an gwamnnati.

Karin bayani