Korea ta Arewa ta harba makamin roka

Makami mai linzami na Korea ta Arewa
Image caption Makami mai linzami na Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta yi gaban kanta, duk kuwa da gargadin da kasashen duniya suka yi mata, ta yi gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango.

Ita dai kasar ta Korea ta Arewa ta ce ta yi nasarar harba tauraron dan Adam a sararin samaniya.

Japan ta ce rokar da aka harba ta wuce ta saman tsibirinta na Okinawa, amma ta yanke shawara kada ta harbo ta.

Sai dai ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zama na gaggawa.

Sakataren gwamnatin kasar ta Japan, Osamu Fujimura, ya ce za su bayyanawa Korea ta Arewa matukar rashin jin dadinsu.

Karin bayani