Gwamnatin Syria na gab da kifewa - Rasha

Syria
Image caption Harin bam ranar Alhamis ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha ya ce mai yiwuwa 'yan tawaye su yi nasarar kifar da gwamnatin shugaba Assad na kasar Syria.

Dakarun Bashar al-Assad "na kara rasa wurare da yankuna da dama da suke iko da su," a cewar Mikhail Bogdanov.

Rasha dai na daya daga cikin kasashen da ke da alaka mai karfi da gwamnatin Assad.

Ko a ranar Alhamis ma, kafafen yada labaran gwamnati sun bayar da rahoton tashin bam a yankin Qatana da ke wajen birnin Damascus.

Amfani da makami mai linzami

Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 ciki harda kananan yara guda bakwai.

Jami'an Amurka da na kungiyar tsaro ta Nato sun ce dakarun gwamnatin Syria na amfani da makamai masu linzami masu cin gajeren zango a fadan da suke yi da 'yan tawaye.

Jami'an, wadanda suka yi magana bisa sharadin ba za a bayyana sunayensu ba, sun ce an harba makami mai linzami samfurin Scud ne daga kewayen birnin Damascus zuwa yankunan da ke hannun 'yan tawaye a arewacin kasar.

Ba tare da ta ambaci makamai masu linzami ba, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland.

Karin bayani