'Yan gudun hijirar Liberia na komawa gida

'Yan gudun hijirar Liberia
Image caption 'Yan gudun hijirar Liberia

Sannu a hankali Liberiya na farfadowa daga yakin basasar da ya daidaita kasar a shekarun 1990.

A watan Yunin bara ne kuma matsayin 'yan gudun hijirar da aka baiwa 'yan kasar wadanda suka tserewa yakin ya kawo karshe a hukumance.

Sai dai har yanzu 'yan gudun hijirar da ke kasashen da ke makwabtaka su kusan dubu ashirin da hudu wadanda kuma suka yi rajistar neman komawa gida tun kafin lokacin suna ci gaba komawa.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ce ke taimakawa tana sake tsugunar da su.

Karin bayani