Sami al Sa'adi na kalubalantar Birtaniya

Sami Al- Saadi

Gwamnatin Birtaniya ta amince ta biya kudi fiye da dala miliyan uku ga wani dan kasar Libya da iyalinsa da suka ce hukumar leken asirin kasar ta MI6 na da hanu wajen azabtar da su domin tatsar bayanai.

Sami al Sa'adi na cikin mutanen da suka bijirewa tsohon shugaban kasar Libya, Kanar Gaddafi kuma ya ce a shekara ta 2004 an tilastawa shi da iyalinsa shiga jirgi daga Hong Kong zuwa Libya inda aka tsare shi kuma aka gana musu azaba.

An dai bankado bayanai dake da alaka da tafiyar ne a lokacin da aka hambarar da gwamnatin kanar Gaddafi a bara, abun da kuma ya sa Mr Al Saadi ya shigar da kara a gaban kotu inda yake tuhumar gwamnatin Birtaniya.

Karin bayani