Jigawa da EFCC suna ta da jijiyar wuya

Gwamnan jigawa Sule Lamido
Image caption Gwamnan jigawa Sule Lamido

Gwamnatin jihar Jigawa a arewacin Najeriya ta maida martani kan kamun da Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yiwa dan gwamnan jihar Alhaji Sule Lamido.

Hukumar ta EFCC ta ce ta kama babban dan Gwamnan, Aminu Sule Lamido ne, saboda zarginsa da take yi da yunkurin fita da kudin da ya haura abin da dokar Nigeria ta kayyade zuwa kasar waje.

Sai dai gwamnatin ta jihar Jigawa ta ce dan gwamnan zai yi amfani da kudin ne don duba lafiyar 'yar sa dake fama da ciwon laka.

Karin bayani