'Yan jarida sun nuna damuwa kan rashin tsaro

Mashawarcin Shugaba Jonathan kan sha'anin tsaro
Image caption Kanar Sambo Dasukl, Mashawarcin harkar tsaro ga Shugaba Jonathan

A kokarin lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa, kungiyar 'yan jaridu ta kasa shiyyar jahar kaduna a arewacin Najeriya ta shirya wani taron tattaunawa wanda ya hada da wasu 'yan siyasa, da 'yan jarida da kuma masana domin duba matsalolin dake haifar da rashin kwanciyar hankali a kasar, musamman ma a arewacin kasar.

Kungiyar ta 'yan jaridun ta shirya wannan taro na tattaunawa ne a cikin jerin shirye -shiryen makon 'yan jarida da take gudanarwa.

Jama'a da dama dai a yanzu a Najeriya na tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda za a kawo karshen zaman zullumin da ake ciki a arewacin Najeriya.

Karin bayani