An saki mahaifiyar Ngozi

Image caption Ngozi Okonjo-Iweala tsohuwar darakta ce a bankin duniya

Rundunar sojin Najeriya da ke jihar Delta ta ce an saki, Farfesa Kamene Okonjo, mahaifiyar ministar kudi ta kasar Ngozi Okonja-Iweala.

Kakakin rundunar sojin Birged ta hudu, Kyaftin Roseline Oluwasewun Managbe, ta ce jami'ansu sun hangi Farfesa Kamene a kan titin birnin Asaba, babban birnin jihar bayan wadanda suka yi garkuwa da ita sun sake ta.

Sai dai ba ta yi karin bayani game da batun ba.

A ranar Lahadi ne wadansu mutane da ba a kai ga gano ko su wanene ba suka yi awon-gaba da Farfesa Kamene Okonjo mai shekaru 82 da haihuwa, a gidanta da ke jihar Delta a Kudu maso Kudancin kasar.

Ranar Alhamis rundunar sojan kasar ta cafke mutane sittin da uku a wani samame da jamiā€™anta suka kaddamar, a kokarin da suke yi na kubutar da Farfesa Kanene Okonjo.

Mai magana da yawun ma'aikatar kudi ta Najeriya ya ce an yi wa Ngozi Okonja-Iweala barazana a baya-bayan nan, amma ba shi da tabbas ko wannan na da alaka da barazanar da aka yi mata.

Karin bayani