Mummunar kiba ta fi kashe mutane a duniya

Image caption Fiye da mutane miliyan uku ne suka mutu saboda mummunar kiba

A karon farko, daya daga cikin manyan bincike-binciken kimiya da aka gudanar ya nuna cewa mummunar kiba ko kuma teba ta fi kashe mutane fiye da rashin samun wadataccen abinci a duniya.

Binciken ya gano cewa mutane fiye da muliyan uku ne suka mutu sabo da mummunar teba a shekara ta dubu biyu da goma.

Wannan adadin ya ninka adadin wadanda yunwa ko karancin abinci kan kashe har sau uku.

Binciken dai ya kwatanta wasu alkaluman bincike ne a shakara ta dubu biyu da goma da kuma wasu bayanan na bincike da aka gudanar kimanin shekaru ashirin da suka gabata lokacin da karancin abinci ya fi kashe mutane fiya da teba.

To sai dai kuma har yanzu karancin abinci da ya dace ya fi kashe mutane fiye da mummunar kiba a Nahiyar Afirka kamar yadda binciken ya nuna.