Babu Rice a takarar sakatariyar wajen Amurka

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Susan Rice
Image caption Rice na fuskantar adawa daga 'yan jam'iyyar Republican

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice, ta janye batun neman mukamin sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Tuni Shugaba Obama ya amince da matakin da ta dauka, amma kuma ya soki abinda ya kira rashin adalci daga bangaren 'yan Jam'iyar Republican ga daya daga cikin jami'an gwamnatinsa.

Mrs Rice ta ce ta janye ne saboda tana kokarin kaucewa yin fito na fiton da zai bata kimar kasarta.

Matakin da Mrs Rice ta dauka na janyewa daga neman wannan mukami, wani babban labari ne a Amurkar, saboda matsayi ne mafi girma a kasar, kana akasari shugaban kasa ne ke zabar wanda zai dora.

Sanata John Kerry

Jakadiya Rice, na shan suka daga kusoshin 'yan jam'iyyar Republican, game da wasu kalamai da ta furta bayan wani hari da aka kai ranar 11 ga watan Satuma kan ofishin huldar jakadancin Amurka a birnin Benghazi dake kasar Libya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jakadan Amurka a kasar, Chris Stephens da wasu Amurkawa uku.

Yanzu dai ya nuna karara cewa Senator John Kerry shi ne ke da tagomashi da aka yi ammanar ke sahun gaba wajen neman wannan mukamin matukar Hillary Clinton ta sauka daga kan mukamin.

Mr Kerry dai ya kasance shugaban kwamitin harkokin kasashen waje a majalisar dattawan Amurkar a cikin shekaru ukun da suka gabata.

Ya kuma rike mukamin manzon musamman ga gwamnatin kasar, wanda ya samu karbuwa daga wasu shugabannin kasashe kamar su Shugaba Karzai na Afganisatan, da ake ganin zai samu goyon baya daga 'yan majalisar dattawan.

Wannan kuwa ya nuna karara cewa shugaba Obama ya dan samu sassauci game da kalubalen siyasar dake gabansa.