An kasa cimma yarjejeniyar shugabanci a harkar Internet

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon
Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon

An kasa cimma yarjejeniya kan batutuwan da suka shafi shugabanci a harkar Internet bayan da aka kwashe kwanaki goma sha daya ana tattaunawa ta kasa da kasa.

Kasar Amurka dai ta ce ba zata sa hannu ba kan yarjejeniyar da suka shafi hanyoyin sadarwa tsakanin kasashen duniya a yadda yake, tana mai cewa yin hakan zai ba gwamnatoci damar sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin sadarwa ta Internet.

Kasashen Burtaniya da Canada da wasu kasashe dabam dabam su ma sun dauki irin wannan mataki a tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta a Dubai.

Kasar Rasha dai ita ce ke jagorantar kasashen da ke adawa da shirin samar da dokoki masu tsauri da suka shafi hanyoyin sadarwa na Internet.