Nijar na bukatar kudi wajan gina Kandaji

Bankin duniya ya tallafa ma janhuriyar Nijar da kudi miliyan 200 na Dollar Amurka, kwatankwacin miliyar 100 na cfa.

Tallafin na daga cikin alkawarin da bankin ya dauka na taimakawa ga ayyukan ginin dam na Kandaji ne, da Nijar din ke ginawa domin samar da wadatar abinci da wutar lantarki.

Tsohon shugaban kasar na Nijar Tandja Mammadou ne ya aza tubalin gina dam din a shekara ta dubu biyu da takwas yayin da shi kuma shugaba mai ci Issoufou Muhammadou ya kaddamar da fara aikin gina shi a shekara ta dubu biyu da goma sha daya da nufin kammala shi a shekara ta dubu biyu da goma sha shida.

Sai dai kuma da wuya hakan ya samu ganin yadda aiki ke tafiyar hawainiya inda mahukunta ke cewa suna fuskantar wasu matsaloli da suka hada da karancin kudi.