An yi hadarin jirgin sama a Bayelsa

Hausa
Image caption Akwai manyan 'yan siyasa da ke halartar jana'iza a jihar ta Bayelsa

Rahotanni daga Najeriya na cewa wani karamin jirgin sama dauke da wasu manyan 'yan siyasar kasar ya yi hadari a jihar Bayelsa da ke Kudu maso Kudancin kasar.

Masu aikin ceto sun ce har yanzu suna ci gaba da yunkurin gano kuraguzan jirgin wanda ya fadi da misalin karfe hudu na yamma.

"Hukumar agaji ta Najeriya NEMA, ta kaddamar da bincike tare da sauran hukumomin agaji domin kai dauki ga wani jirgin sama da ake tunanin ya fadi a jihar Bayelsa," kamar yadda mai magana da yawun hukumar Yusha'u Shuaib, ya shaida wa BBC.

Manyan 'yan siyasa da dame ne suka halarci jana'izar mahaifin Oronto Douglas a garin Nambe na jihar ta Bayelsa.

Wasu rahotanni da ba'a tabbatar ba, sun ce jirgin ya fadi sannan ya kama da wuta, kuma babu tabbas kan halin da wadanda ke cikin jirgin suke.

Batun hadarin jiragen sama ba bakon abu bane a Najeriya.

A watan Maris, wani karamin jirgin sama na 'yan sanda dauke da wani babban jami'in 'yan sandan ya fadi a garin Jos, inda mutane hudu suka mutu.

Wani jirgin fasinja ma ya fadi a wata unguwa mai cike da dinbin jama'a a watan Yuni, a jihar Legas, inda ya kashe mutane 163.

Muna dauke da karin bayani

Karin bayani