'Yan siyasa sun bukaci dokar hana mallakar makamai a Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

'Yan siyasa da dama har da shugaba Barack Obama sun yi kiran daukar tsauraran matakai domin hana sake abkuwar wannan lamari nan gaba.

Wannan kuwa ya biyo bayan kisan da wani dan bindiga ya yiwa kananan yara 'yan makarantar firamare a dan karamin garin Newton dake jihar Connecticut, arewa maso gabashin Amurka.

Kisan wanda shine mafi muni na baya-baya a tarihin Amurkar da aka bayyana, ka iya tada zazzafar muhawara akan dokar mallakar bindiga a Amurkar.

Dokar haramta amfani da kananan bindigogi ya kasance abu mai cike da kace-nace a Amurka, wacce 'yancin mallakar makamin na kunshe a cikin kudin tsarin mulkin kasar.

To sai dai tsaurara dokar mallakar bindiga a Amurka wani batu ne mai sarkakiya kasancewar 'yancin mallakar makami na kunshe ne a kundin tsarin mulkin kasar.

Wani dan Majalisa dan Jam'iyar Democrat Jerrold Nadler, ya ce idan yanzu lokaci bai yi ba na a tattauna game da wannan batu, to kuwa bai san sai lokaci ne cancata ayi hakan ba.

Yayinda dai cikakkun bayanai game da wannan abin firgici na baya-bayan nan da ya faru a Amurkar, an fara muhawara game da hanyoyin da suka kamata a bi wajen shawo kan matsalar.

Obama ya jaddada daukar matakai

Shugaba Barack Obama wanda ke cike da damuwa ya ce kasar wacce ta dade tana fama da irin wadannan matsaloli na kashe-kashe masu kama da wannan, nan bukatar daukar matakai masu tsauri.

Magajin Garin New York, Michael Bloomberg, ya yi Allah wadai da abinda ya kira rashin shugabanci tun daga fadar White House har ya zuwa majalisa game da batun.

A shekarar 1994 a zamanin mulkin Bill Clinton ne dai aka haramta amfani da kananan bindigogi, sai dai dokar haramcin ta kare ne bayan shekaru 10 lokacin da shugaba George W Bush ke mulki.

Kimanin shekaru 5 kenan da wani dalibi a jami'ar Fasaha ta Virginia hallaka mutane 32 ya kuma raunata mutane 15.

A watan Yulin wannan shekarar wani mutum daya lullube fuskarsa ya hallaka mutane 12 kana ya raunata mutane 50 a gidan Sinima dake Aurora a jihar Colorado.

Galibin Amurkawa har yanzu na amannar cewa mallakar bindigogi abu ne da kudin tsarin mulkin kasar ya yarje musu.

Hakan kuwa na nufin idan dai har shugaba Barack Obama ya bukaci doka mai tsauri game da mallakar makaman, zai iya fuskantar kalubale a kama daga majalisa har ya zuwa kotuna.