Neman sauya dokar mallakar bindiga a Amurka

Tutocin Amurka
Image caption An yi kasa-kasa da tutocin Amurka

An sassauto da tutoci kasa-kasa a sassa da dama na Amurka, bisa umurnin shugaba Obama, bayan daya daga cikin hare haren bindiga mafiya muni da aka taba kaiwa a tarihi a Amurkar.

Yara kanana da wasu magidanta ashirin da shidda ne aka bindige har lahira a wata makarantar firamare a jihar Connecticut, jiya Juma'a.

'Yan siyasa da dama ciki har da shugaba Obama sun bukaci a bullo da sauye sauye a dokokin mallakar bindigogi na Amurkar domin kauce ma aukuwar irin wannan bala'i a gaba.

Masu zanga zanga da dama sun taru a gaban fadar White House suna bukatar a dauki mataki nan take.

Sai dai kuma duk da irin harbe harbe masu kama da wannan da aka yi ta yi a shekaru biyun da suka wuce da ba wani kwakkwaran mataki da ake san a dauka dangane da hana afkuwar hakan.

Ganin a na samun karuwar cikakkun bayanai game da harbe-harbe na baya-bayanan,mahawara na zafafa kan hanyoyin da ya kamata abi domin shawo kan matsalar.

Shugaban Barack Obama ya nuna karara cewa, wannan abu ya yi yawa a kasar, kuma akwai bukatar a dauki matakai masu fa'ida a kanshi.

Magajin garin New York, Micheal Bloomberg, ya yi Allah wadai kan abun da ya kira rashin daukar matakan da suka dace daga bangaren fadar White House zuwa majilasa kan lamarin.

Daga na shi bangare gwamnan jahir Colorado, ya ce maganar harbin jama'a da dama a lokaci guda na watan Yuly, ba magana ce ba da ya kamata a dage yin ta ,magana ce da ya kamata a ci gaba da tautaunawa a kai, domin lamarin na faruwa lokaci zuwa lokaci.

Karfin da dokar take da shi dai ya fara rage tagomashi kwarai a cikin yan shekarunan, ganin cewa kisan kai na ci gaba da karuwa.

Yawancin Amurkawa na da tunanan cewa mallakar bindiga abu ne da tsarin mulki ya bayar da izine a kai.

Yawancin yan siyasa ba sa son a dau mataki kan lamari duk da cewa su na da massanniya kan abun da ke faruwa, sabili da gani su ke abu ne mai hadari.

Idan Barack Obama na sun karfafa dokoki kan wannan lamari, ga dukan alamu zai fuskanci turjiya da gwagwormaya daga bangaren majilasa da kuma kotunan kasar.

Karin bayani