Gwamnan Kaduna Patrick Yakowa ya rasu

Patrick Yakowa
Image caption Najeriya na da mummunan tarihi wurin hadarin jiragen sama

Rahotanni daga Najeriya na cewa gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan al'amuran tsaro Janar Azazi, sun mutu a wani hadarin jirgin sama a jihar Bayelsa.

Wata sanarwa da jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya da kuma jihar ta Kaduna ta fitar, ta bayyana ta'aziyyarta ga mutuwar gwamna Patrick Yakowa da kuma sauran manyan 'yan Najeriya da suka mutu tare da shi, ciki harda tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan al'amuran tsaro Janar Azazi.

Editan BBC na Abuja Bashir Sa'ad Abdullahi, ya ce manyan 'yan siyasa da dame ne suka halarci jana'izar mahaifin Oronto Douglas a garin Nambe na jihar ta Bayelsa, ciki har da gwamnan jihar Kaduna Patrick Yakowa, da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan al'amuran tsaro Janar Owoye Azazi.

"Wani karamin jirgin sama na rundunar sojin nruwa ta Najeriya dauke da mutane bakwai ya yi hadari a jihar Bayelsa, da misalin karfe hudu na yamma," a cewar mai magana da yawun rundunar sojin ruwa ta Najeriya.

"Hukumar agaji ta Najeriya NEMA, ta kaddamar da bincike tare da sauran hukumomin agaji domin kai dauki ga wani jirgin sama da ake tunanin ya fadi a jihar Bayelsa," kamar yadda mai magana da yawun hukumar Yusha'u Shuaib, ya shaida wa BBC.

Yawan hadarin jirgin sama

Wasu rahotanni sun ce jirgin ya fadi ne sannan ya kama da wuta, kuma dukkan wadanda suke cikin jirgin sun rasa rayukansu.

Batun hadarin jiragen sama ba bakon abu bane a Najeriya.

A watan Maris, wani karamin jirgin sama na 'yan sanda dauke da wani babban jami'in 'yan sandan ya fadi a garin Jos, inda mutane hudu suka mutu.

Wani jirgin fasinja ma ya fadi a wata unguwa mai cike da dinbin jama'a a watan Yuni, a jihar Legas, inda ya kashe mutane 163.

Karin bayani